A makon da ya gabata aka sauya jadawalin ziyarce-ziyarcen shugaban na Amurka saboda guguwar Milton da ta afkawa jihar Florida
Kalaman manyan 'yan takarar biyu na zuwa ne yayin da Amurkawa ke shirin kada kuri'a a ranar 5 ga watan Nuwamba.
Kalaman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke kai hari kan mayakan Hezbollah a Lebanon da sabunta hare-haren da take kai wa kan Hamas a arewacin Gaza.
Wani rahoto da asusun na UNICEF ya fitar, ya bayyana cewa 1 daga cikin kowadanne yara mata 8 a duniya suna fuskantar hadarin cin zarafi da fyade. Daya daga cikin matan 5 kuma suna fuskantar irin wannan barazana ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani, wanda adadinsu ya kai miliyan 650.
Tsarin makami mai linzamin na’ura ce ta kasa wacce aka kera don kare kariya daga makamai masu linzami kirar ballistic.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ta bada rahoton cewa, akalla mutane 10 ne suka mutu, sannan masu aikin ceto suna ci gaba da ceto wadanda suke raye, amma mutane da dama sun bayyana farin ciki cewa Milton bata yi muni sossai ba.
Guguwar ta lalata gidaje kuma ta kashe akalla mutum biyar tare da barin mutane miliyan uku ba wutar lantarki kafin daga bisani ta koma Tekun Atlantika.
An yi gargadin yiwuwar samun ambaliya a daren Laraba ga kusan dukkan gabar yammacin yankin Florida, wanda ya kai tsawon kilomita 500.
Biden ya yi alkawarin kai ziyara nahiyar Afirka yayin wa’adin mulkinsa, wanda zai kare a watan Janairu.
A yayin ganawar da tayi da Amurkawa musulmi yan asalin kasashen larabawa, Kamala Harris ta jaddada kokarin da gwamnati keyi na kawo karshen yakin da ake yi a Gaza da Lebanon, tare da samar da kariya ga farar hula.
Shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris sun yi balaguro a ranar Laraba, inda suka kai ziyara yankunan kudu maso gabashin Amurka, don gane wa idanunsu irin baranar da guguwar Helene ta yi.
Abokan takarar biyu sun amince cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke cikin Amurka ba bisa ka’ida ba babbar matsala ce.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.