Masu zanga-zanga a Isra’ila sun toshe manyan tituna tare da kutsawa cikin kasuwar hada-hadar hannayen jari , yayin da ‘yan majalisar dokoki ke shirin amincewa da daya daga cikin kudurorin dokar shari’a na Firai minista Benjamin Netanyahu da ake takaddama a kai.
Yau aka fara gudanar da taron Amurka da kasashen Afrika a birnin Gaborone na kasar Botswana karo na 15 wato US Africa Business Summit.
Ofisoshin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Lagos sun gudanar da wani Kwas na wayar da kan daruruwan daliban Najeriya da su ka sami guraben karatu a jami'o'i da kwalejojin Amurka
Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta, ya kaddamar da sabuwar manhajar sa ta Threads, manhajar sada zumunta da ke da nufin yin adawa da shaharar manhajar Twitter malllakar daya daga cikin masu kudin duniya Elon Musk.
An fuskanci wani yanayin zafi da ba a taba samun irin sa ba cikin shekaru a kasashen duniya a ranar Talata wanda ranar Laraba na iya zama rana ta uku a jere da za a yi fama da wannan zafi da ya kafa tarihi a duniya.
Rundunar sojojin ruwan kasar China na yin wata ziyarar aiki a Najeriya cikin wannan makon, a wata ziyara da ba a saba gani ba a yammacin Afirka, inda China ke neman fadada tasirinta.
Harbin Da aka yi a wurare daban-daban a Philadelphia, Baltimore da Fort Worth gabanin bukin ranar ‘yancin kan Amurka da akayi a ranar Talata, ya haifar da sabbin bukatu ga shugaban Amurka Joe Biden na samar da dokar mallakar bindigogi.
Shahararriyar mawakiyar ta bayyana hake a shafinta na sada zumunta inda ta ce tana kaunar fitaccen mawakin Rema.
An zabi Burna a rukunin BET tare da Aya Nakamura, Ayra Starr, Central Cee, Ella Mai, KO, L7nnon, Stormzy, Tiakola da kuma Uncle Waffles.
A wata ziyara da suka kai ranar Litinin 19 ga watan Yuni 2023, hamshakin attajirin duniya Bill Gates da hamshakin dan kasuwa Aliko Dangote sun kai wa shugaba Tinubu ziyara a fadar shugaban kasa.
Shugaban kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL, Mal. Mele Kyari ne ya bayyana hakan a a yayin ganawa da mataimakin sakataren makamashi na kasar Amurka, Geoffrey Pyatt, a wata ziyarar da ya kawo ma gwamnatin tarayyar kasar a birnin Abuja.
Shugaban Gidauniyar Bill and Melinda Gates, wato attajirin nan na kasar Amurka, Bill Gates da attajirin Najeriya kuma shugaban gidauniyar Dangote Foundation, Aliko Dangote sun yi rangadi a jamhuriyar Nijar yau Litinin 19 ga Yuni, 2023 inda suka gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.