Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Jamhuriyar Nijar a yau Alhamis 16 ga watan Maris inda zai tattauna da takwaransa Hassoumi Massaoudou ( Hasumi Masa’udu) kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu masu dadaddiyar huldar diflomasiya.
Takwas ga watan Maris din kowace shekara, rana ce da ake bikin mata ta duniya inda taken bana ya mai da hankali kan bukatar samar da daidaito a tsakanin jinsi.
Jami'ar gwamnatin Biden da ke da alhakin kula da sojojin Amurka ta bayyana dabarun dakile duk wata barazanar yaki, tare da yin nasara daga kasar China, idan bukatar hakan ta zo.
Kwanaki biyu gabannin babban zabe a Najeriya, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gudunar ta taron mata zalla don wayar da kansu da kuma ilimantar dasu game da zaben, ganin cewa mata sune suka fi yawa wajen kada kuri’a a lokacin zabe bisa la’akari da zabukan baya.
Hukumar kula da kafafen labarai na ketare ta Amurka wato USAGM, ta hori wakilan kafafen labaru na Najeriya kan yadda za su tsare dokokin aikin jarida idan sun tashi ba da labarai kan yadda za a gudanar da babban zabe har zuwa bayan sanar da sakamako.
A shekarar 2000 aka kebe ranar 21 ga Fabrairu, a matsayin ranar bukin harshen uwa ta duniya (IMLD).
A ciki da wajen birnin New Orleans na jihar Louisiana da ke Amurka, ranar Talata ne za a gudanar da babban bikin Mardi Gras, lokacin bukukuwa na tsawon makonni da aka saba yi a al’adance.
“Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowane ‘dan takara a zaben Najeriya. Ta ce ita dai babban muradinta shi ne ta ga an gudanar da ingantaccen zabe, na gaskiya mai cike da adalci, wanda kowa da kowa zai na'am da shi”
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a jiya Talata cewa, labarin Amurka labari ne na ci gaba da jajircewa, yayin da yake jawabi a kan halin da kasa ke ciki da ya maida hankali a kan manufofin tattalin arzikin na cikin gida, inda ya kara da kira ga ‘yan adawa na Republican da su hadu su yi aiki tare.
Sojojin Amurka sun ce sun kakkabo wannan baban bala-balan din kasar China na leken asiri a yankin gabar tekun Carolina.
A wani mataki na nuna goyon baya ga tsarin dimokaradiyya a Naijerya, Amurka ta sanya takunkumin bulaguro ga mutanen da ke da hannu wajen yin zagon kasa ga dimokradiyya a Najeriya
An zabi Temilade Openiyi, wacce aka fi sani da Tems, a jerin sunayen fitattun ‘yan wasan fina finai na lambar Yabo ta Oscars 2023, saboda gudunmawar da ta bayar a rubuta wakar da ake kira ‘Lift Me Up’, daya daga cikin wakokin sauti na wani fitaccen silma na Marvel’ Black Panther: Wakanda Forever.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.