Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bikin Ranar Mata A Duniya 


Pakistan International Women's Day
Pakistan International Women's Day

Takwas ga watan Maris din kowace shekara, rana ce da ake bikin mata ta duniya inda taken bana ya mai da hankali kan bukatar samar da daidaito a tsakanin jinsi.

WASHINGTON, D.C. - Bikin na shekara-shekara, wanda aka fara shi a shekara ta 1911 da hanyar fafutukar kwato 'yancin mata, rana ce da jama'a a ko'ina suke biki don murnar nasarorin da mata suka samu a cikin al'umma.

Montenegro International Women's Day
Montenegro International Women's Day

Majalisar Dinkin Duniya a wannan karon ta karkata shirye-shiryenta na ranar mata ta duniya kan muhimmancin kare hakkin mata da 'yan mata a sararin intanet ko a yanar gizo da kuma yin aiki don ganin saukin samun kayan muhimman fasahohi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a duk fadin duniya mata kasa da miliyan 259 ne ke samun damar amfani da intanet akan maza, kuma ba tare da samun damar shiga yanar gizo ba, ba za su iya koyan dabarun da za a dama da su a fagen fasahar sadarwa ta zamani ba.

Afghan International Women's Day, in Kabul, March 8, 2023.
Afghan International Women's Day, in Kabul, March 8, 2023.

A Washington, babban birnin Amurka, a karon farko, ana gudanar da bikin da karrama mata masu jaruntaka na duniya a fadar shugaban kasa ta White House.

Kyautar wacce aka baiwa mata 180 daga kasashe 80 tun daga shekara ta 2007, “tana ba da lambar yabo ga mata daga ko'ina cikin duniya waɗanda suka nuna jajircewa, ƙarfi, da jagoranci na musamman wajen ba da shawarar samar da zaman lafiya, adalci, 'yancin ɗan adam, daidaiton jinsi, wanda yake galibi da babban haɗari da sadaukarwa,” a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.

WOMENS-DAY/GERMANY
WOMENS-DAY/GERMANY

Bikin na bana zai kunshi mutane 12 da za a karrama, ciki har da lambar yabo ga mata da 'yan mata a Iran wadanda suka jagoranci zanga-zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini a watan Satumba a hannun 'yan sanda.

-Reuters

XS
SM
MD
LG