Daruruwan dubban Falasdinawa ne suka rasa gidajensu sanadiyyar hare-haren saman da Isra’ila take kai wa kan Hamas a matsayin martanin harin da ta kai wa Isra’ilan.
Magajin garin Newark, New Jersey a Amurka, Ras J. Baraka, ya karrama Kanyeyachukwu Tagbo Okekene a ranar Lahadi da lambar yabo, a yayin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya karo na 8 a jihar.
“Alamu sun nuna karara cewa yanzu ba lokacina ba ne.” In ji tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence.
Hukumomin jihar sun ce mutunin da ake zargi da yin harbin ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji daga harbin bindigar da yayi wa kansa.
An rufe dukkan makarantun gwamnati da ke kusa da Lewinston a ranar Juma’a yayin da hukumomin ke ci gaba da farautar mutumin wanda ake kira Robert Card.
Wani babban jami’in sojin Amurka ya fadawa manema labarai cewa jiragen yaki kirar F-16 ne suka kai takaitaccen harin a wani rumbun adana makamai a kusa da Abu Kamal.
Amurka ta dakatar da galibin tallafin kudi ga kasar Gabon da ke tsakiyar Afirka a matsayin mayar da martani ga juyin mulki da sojoji suka yi a watan Agusta.
Hakan dai na nufin an koma gidan jiya yayin da majalisar ta kwashe makonni babu tsayayyen shugaban da zai jagorance ta.
A Tel Aviv, shugaban Amurka Joe Biden ya dora alhakin fashewar da auku a Asibitin Gaza a kan dayan bangaren.
Shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Isra'ila da Jordan ranar Laraba domin ganawa da shugabannin Isra'ila da na Larabawa, yayin da ake fargabar cewa yakin Isra'ila da Hamas zai iya kazance wa ya mamaye yankin.
Dubban jama'a ne a wata unguwar Falasdinawa da ke birnin Chicago a ranar Litinin suka gudanar da jana’iza da karrama wani yaro Musulmi dan shekara 6 da aka kashe a wani yanayi da ake zargi na nuna kyamar Musulunci ne.
Gwamnatin jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta soma wani yunkuri domin ganin jama’ar jihar sun amfana da ilmi, arziki, wayewa da fasahar ‘yan asalin jihar da ke zaune a Amurka da ma sauran kasashen duniya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.