Daya daga cikin bayanan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken yayi a ziyarar da ya kai Najeriya shi ne albishir da ya yi wa kasar na cire sunanta daga jerin kasashen da ke tauye 'yancin addini, batun da ya dauki hankalin al'umma.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaye kallabin sababbin kudurorin Amurka sa'adda yake jawabi ga jami'an diflomasiyya da na gwamnatoci a sakatariyar kungiyar raya kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ya ke ci gaba da ziyara
Amurka da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tare a bangarori da dama, inda kasar ta Amurka ta yi alkawarin taimaka wa Najeriyar wajen shawo kan wasu daga cikin dinbin matsalolin da take fuskanta.
A cigaba da ziyarar Afurka da ya ke yi, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya isa Najeriya, inda zai dada bayyana manufofin Amurka game da Afurka.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya isa kasar Kenya, kasa ta farko da ya yada zango a ziyarar kasashen Afrika uku da zai kai wannan makon.
Janar Colin Powell, wanda shi ne bakar fata na farko da ya rike mukamin Sakataren harkokin wajen Amurka ya mutu ne a ranar Litinin bayan fama da cutar COVID-19. Shekarunsa 84.
Powell ya rike mukamin sakataren harkokin wajen Amurka a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2005 a wa’adin farko na shugaba George W. Bush.
A ranar Talatar makon jiya ne shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatoci suka fara jawabai a mahawarar babban taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na cikon shekaru 76 a birnin New York.
Shugabannin kasashen Afurka da dama ne suka yi jawabansu a rana ta biyu a taron kolin na Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai bayanan shugabannin sun fi maida hankali ne a kan batun coronavirus da batun raba rigakafin annobar daidai tsakanin kasashe.
Dukkan shugabannin suna fara jawaban su ne da batun annobar coronavirus da ta hana gudanar da taron na gaba da gaba a bara da kuma yanda annobar ta kawo nakasu ga shirin muradun karni da ma tattalin arzikin duniya.
Taron na wannan shekara ya banbanta da yadda aka saba gani a shekarun baya, inda dubban mutane ke halartar wannan taro dake tattaro shugabannin kasashe da firai ministoci da manyan tawagogi da kuma wakilai na kungiyoyi masu zaman kansu zuwa nan birnin New York.
Taliban ta mulki Afghanistan daga 1996 zuwa 2001 inda ta gudanar da mulkinta karkashin shari’ar Musulunci a kasar. Ga wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka shafi akida da tarihin kungiyar.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.