Wannan kuwa wani bangare ne na ziyarar da Sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ke yi a Najeriya, inda tuni ya gana da shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan jami'an gwamnati.
A jawabinsa kafin sa hannu a yarjejeniyar, Sakatare Blinken ya bayyana matsayin Najeriya a harkokin kasashen waje da kuma Amurka. A ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari, Blinken ya ce, Amurka ta maida hankali wajen kulla yarjejeniyar dangantakar diflomasiya da wadansu al'amura da dama da ake kyautata zaton za su amfani kasashen biyu musamman Najeriya da ke matsayin kasa mai tasowa.
Sha'anin annobar korona ne ya zama batu da aka sa gaba a tattaunawar, inda sakatare Blinkin ya ce tuni Amurka ta ba Najeriya gudummuwar allurar rigakafin annobar korona miliyan bakwai da dubu dari shida. Sakataren harkokin wajen Amurkan ya kuma bayyana cewa,ana sa ran kara kawo rigakafin kafin karshen wannan shekarar ta dubu biyu da ishirin. Blinkin ya bayyana cewa, Amurka ta yi aikin hadin gwiwa da Najeriya wajen yaki da cutar Korona. Lamarin da ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
A bangaren tsaro kuma Sakatare Blinkin ya ce Amurka tana aiki da Najeriya wajen yaki da kalubalen tsaro kama daga yaki da kungiyar Boko Haram da kungiyar ISIS ta yammacin Afrika, wanda ya ce shi da mataimakin shugaban Najeriya sun amince cewar, yana bukatar kwakkwaran shiri da tanadi da ya kunshi samar da ingantacciyar rundunar soji, da magance tsatsa-tsauran ra'ayin addini da mutunta haki da 'yancin 'yan kasa.
Sakataren harkokin wajen Amurkan ya ce Amurka ta kuduri aniyar taimaka wa Najeriya wajen cimma wannan manufa ta hanyar hadin gwiwar samar da tsaro, da karfafa doka da oda, da hukumta dukan masu take hakin bil'adama, da cin hanci da rashawa, da kuma duk ayyukan da ka cutar da 'yan Najeriya.
Sauran muhimman batutuwan da aka tattauna sun hada da inganta harkokin ilimi, da kiwon lafiya da tada komadar tattalin arziki, kazalika da kuma shawo kan matsalar gurbatar yanayi, da Amurka ta jinjinawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan kudurorin gwamnatinsa da ya gabatar a taron da ya gudana kan sauyin yanayi.
Da yake maida martani a madadin gwamnatin Najeriya, Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, ya ce tattaunawa tsakanin Amurka da Najeriya ta baya bayan nan, ta soma ne tun haduwar shugabannin biyu a taron sauyin yanayi da aka gudanar a Glasgow , inda shugaba Joe Biden ya yi alkawarin tallafawa Najeriya, wajen shawo kan dimbin matsalolin da ta ke fuskanta.
Ministan harkokin wajen Najeriyan ya bayyan burin ganin hadin guiwar ya taimakawa wajen magance matsaloli da kasashe masu tasowa irin Najeriya su ke fuskanta. Ya kuma bayyana farin cikin ganin yadda wannan batun ya zama tsari da manufofi na zahiri na gwamnatin Amurka.
Ko baya ga tattaunawa da shugaba Buhari, sakatare Blinkin ya kuma gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, inda suka rattaba hannu a kan wadansu yarjejeniyoyin aiki tare. A yayinda su ka rattaba hannu a kan
Sakare Blinkin ya isa Najeriya ne kasa ta biyu a ziyarar kwanaki biyar da za ta kai shi kasashen nahiyar Afrika uku da suka hada da Kenya, Najeriya da kuma Senegal da ta kasance kasa ta uku da zai kai ziyara.
Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna cikin sauti: