Ranar 13 ga watan nan na Afirilu, Muryar Amurka zai saki wani bidiyo da zai nuna fuskokin manyan mayakan kungiyar Boko Haram a wani hoton bidiyo da suka da kansu, wanda ya mu shigo wa hanun Muryar Amurka. Ga somin tabi.
'Yan kunar-bakin-waken da ake kyautata zaton cewa 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan wasu sansanonin 'yan gudun hijira dake kusa da tashar motar Muna a Maiduguri, cikin daren da ya shige.
A lokacin da 'yan Boko Haram suke cin karensu babu babbaka, ga wani bidiyo nasu da ya nuna yadda suke sauke babura ko mashina a kofar gidan shugabansu a garin Kumshe sai dai ba a san inda suka samo wadannan babura ko mashina ba, wadanda sabbi ne ful a cikin kwalayensu.
A wannan bidiyo, Khalifa Aliyu Ahmad Abulfathi zai yi bayani kan mummunar akidar kungiyar Boko Haram da irin ta’asar da suka yi a lokacin suna ganiyar kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.
A wannan bidiyo za ku kalli yadda ‘yan kungiyar Boko Haram suke gudanar da atusaye da motsa jiki a wani yankin arewa maso gabashin Najeriya da suka karbe ikonsa a lokacin suna ganiyar cin karensu ba babbaka a tsakanin shekarun 2014 da 2015. A yi kallo lafiya.
A wannan hira da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya yi da Muryar Amurka, ya bayyana irin nasarar da aka samu akan kungiyar Boko Haram tun bayan da gwamnatin shugaba Muhamamd Buhari ta karbi ragamar mulki tare da bayyana irin kalubalen sake gina yankin dake gaban gwamnatin jiha da ta tarayya.
A wannan bidiyo, za ku kalli fatawar da Sheikh Duguri ya bayar kan ma’anar kalmar jihadi, inda ya nuna cewa irin jihadin da ‘yan kungiyar Boko ke ikrarin suna yi ya sabawa koyarwar addinin Islama.
Muryar Amurka ta leka wani sansanin ‘yan gudun Hijira dake garin Bama da ya yi fama da hare-haren kungiyar Boko Haram. A wannan bidiyo za ku kalli yadda yara ke zuwa makaranta da kuma yadda ake kokarin samar da ababan more rayuwa a wannan sansanin.
Lokacin da Muryar Amurka ta ziyarci garin Bama dake Jihar Maiduguri, mun zanta da wasu mazauna garin inda suka mana bayani kan yadda ‘yan kungiyar Boko Haram suka rika harbi tare da jefa mutane cikin ruwa daga kan Gadar Bama a lokacin suna rike da ikon garin.
A wannan karon za ku kalli yadda kungiyar Boko ta ke kai hare-hare a duk lokacin da ta bushi iska, a yankin arewa maso gabashin Najeriya a tsakanin shekarun 2014 da 2015, kamar yadda hoton bidiyo da suka dauka da kansu ya nuna.
A ci gaba da kawo maku faya-fayen bidiyon ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram, tsarabarmu ta yau ta kunshi yadda kungiyar ta ke shirya farfagandarta. A yi kallo lafiya.
A wannan bidiyo za ku kalli hirar wasu makiyayi da Muryar Amurka inda suka ba da labarin yadda suka gujewa yankunansu saboda addabarsu da ‘yan kungiyar Boko Haram ke yi da sace-sace shanu a garinsu na Dar Gemal.
Domin Kari