A daidai lokacin da jama'a kasar Nijar ke jiran sakamakon zabukan da suka yi da za'a bayya yau karfe biyar agogon Niamey, Muryar Amurka ta zagaya ta ji ra'ayoyin mutane.
Kamar yadda wakilinmu ya gano an dauki tsauraran matakan tsaro a babban birnin kasar a wani shirin ko ta kwana da gwamnatin kasar ta yanzu ta yi.
Wakilinmu ya zanta da shugaban malaman addinin Musulunci na kasar Shaikh Jebril Makil wanda ya kira al'ummar kasar su nemi zaman lafiya. Yace musulmi ya kamata ya sani cewa duk abun da auku daga Allah ne. Ya kamata su amince da abun da Allah ya yi. Ya kira mutane kada su mance da kasarsu. Kada su mance da al'adar Nijar wadda ita ce kwanciyar hankali. Nijar bata saba da tashin hankali ba.
Shugaban musuluncin ya kira 'yan siyasa da suka yi nasara su yi adalci wadanda kuma basu samu nasara ba su yi hakuri. Yace a bar fitina saboda Allah ya yi tur da wanda ya tada fitina.
Da ya koma kan matasa sai yace su yi hankali domin su ne ake ingizawa gaba su tada fitina. Yace su kiyaye domin idan kasar ta gyaru tasu ce.
Shaikh din ya kaiwa jam'an hukumar zabe Kur'ani da suka rantse dashi cewa zasu aikata gaskiya saboda haka bashi da shakka zasu aikata gaskiya.
Shi ma wani shugaban addinin Kirista Fasto Lawali Garba yace bayan an bayyana sakamakon zabe jama'a su karba su kuma rungumi zaman lafiya domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Kada su yi tashin hankali domin tashin hankali koma baya yake kawowa.
Dangane da 'yan siyasa ya kirasu su karbi sakamakon. Wadanda suka ci su yi adalci wadanda basu ci ba su jira nasu lokacin. Allah ne ke ne ke bada mukami a koyaushe ya ga dama ga wanda ya ga dama.
Ya kira matasa kada su bari a karkata karfinsu da hazakarsu zuwa aikata tashin hankali.
Ga karin bayani.