A firar da abokiyar aiki tayi da Malam Rafsanjani ya bayyana banbancin dake akwai a zaben bana da wadanda aka saba gani can baya.
Wasu mazauna birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyon Najeriya sun bayyana ra'ayinsu akan zaben shugaban kasar Amurka musamman akan 'yan takaran dake kan gaba wato Hillary Clinton da Donald Trump
Yayin da ake shirye shiryen gudanar da babban zaben shugaban kasa a Amurka, biyo bayan yawan kamfen da ‘yan tarar shugabancin kasar ke yi na ganin sun sami nasara a zaben da za a yi gobe Talata.
Baki daya ‘yan takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat da Donald Trump na jam’iyyar Republican sun mayar da hankalinsu akan wasu jihohi da suke bukatar ganin sun sami nasara a kansu.
'Yar takarar shugabancin Amurka Hilary Clinton da Donald Trump duk sun gudanar da gangamin yakin neman zabe jiya Alhamis da dare a jahar Carolina ta Arewa-jahar da kusan tilas duk mai tsammanin zama shugaban Amurka tsakaninsu ya sami nasara zaben da za'a yi ranar Talata idan Allah Ya kaimu.
Hillary Clinton da Donald Trump basu yi kwauron baki ba a yayin da ratar dake tsakanin su a kuri’ar gwaji ke kara tsukewa, dukkan su Yan takarar na kokawar samun damar cin zaben dake kara matsowa.
Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amura FBI ta sami izinin kotu don bincikar wasikun email din Hillary Clinton. Sai dai kuma 'yan jam'iyyar Democrat na ganin akwai muna kisar siyasa.
Yar takara shugancin kasa a nan Amurka karkashin jami’iyar Democrats Hillary Clinton ta ninka abin da abokin karawarta na Republican Donald Trump yake kashewa na zunzurutun kudade a gwagwarmayarsu ta shiga fadar White House.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jami’iyar Republican Donald Trump, wanda ke dada fuskantar matsaloli a kokarin da yake na lashe zaben, yanzu ya juya yana zargin abokiyar karawarsa Hillary Clinton da cewa tana shirya tattara ra’ayoyin jama’a na karya don aga tamkar itace kan gaba.
Tattaunawa Da Amsa Tambayoyinku Kan Zaben Amurka 21-10-2016
Shugaba Barack Obama na Amurka yace nacewar da dan takaran jam’iyyar Republican azaben bana a nan Amurka, Donald Trump ke yi na cewa za’ayi mishi magudi a lokacin zaben, ba “abin dariya” bane.
Domin Kari