Tsohon abokin takarar Hillary Clinton a zaben share fage, Senata Bernie Sanders shine ya gabatar da ita A gangamin data yi a birnin Raliegh, yayin da abokin hamayyarta na jam'iyyar Repuvblican Donald Trump yake nasa gangamin ba nesa daga inda take, inda yayi magana ga gungun mutane masu ra'ayin soja a birnin Selama.
Dukkansu biyu sun nanata caccakar da ske yiwa juna cewa dayan bai cancanci rike shugabancin Amurka ba, yayinda suke kara kira ga magoya bayansu su sani cewa kuri'unsu suna da tasiri.
Tun farko a wani gangamin da tayi a birnin Greenville a jahar ta Carolina ta Arewa, Clinton ta gargadi jama'a su san cewa "a kullum fa mutum na farko da Trump yake sawa gaba shine Trump, kuma bai damu da duk wadda hakan zai yiwa illla ba."
Babban mai goyon bayanta shugaba Obama yayi mata yakin neman zabe a jahar Florida, wacce tilas masu neman shugabancin na Amurka su sami nasara.
Sakamakon wasu sabbin kuri'ar neman ra'ayin jama'a sun nuna ncewa Hillary tana gaba da Trump, a binciken da jaridar New York Times da tashar talabijin ta CBS suka gudanar ya nuna Clinton tana da maki 45 yayinda Trump yake da maki 42. Wacce jaridar Washington Post da tashar talabijin ta ABC suka gudanar ya nuna tana da kashi 47- Trump kuma yana da kashi 45.