Masu zanga zangar dai na nuna kin jinin sabon zabebben shugaban ne Donald Trump a zaman mai akidar wariyar launin fata kuma wanda ya tsana ko yake da ra’ayin danne hakkin mata, sun yi zanga-zanga a titunan birane da dama a nan Amurka domin nuna Rashin jin dadin nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa.
Mutane masu yawa sun cika titin Fifth Avenue na birnin New York, daidai gaban ginin Trump Tower, inda zababben shugaban yake zaune, dauke da kwalayen dake cewa “Soyayya ta fi Kiyayya.” Kalmar “ta fi” din a turance dai it ace Trump, watau suna amfani da sunansa.
Wasu gungun jama’a kuma sun taru a gidan da Trump yake shirin shiga, watau Fadar White House a nan Washington. A dai nan kan titin Pennsylvania Avenue a sabon hotel na Trump da aka bude, masu zanga zanga sun taru suna cewa “Ku Fada da karfi, kuma a fili: Muna marhabin da ‘yan gudun hijira a nan.”
A wasu sassan nan yankin gabashin Amurka, an gudanar da zanga zanga a biranen Miami a jihar Florida, da Philadelphia a jihar Pennsylvania da kuma Boston a Jihar MA inda ‘yan zanga zan ga suka rike kwalayen dake kiran da a tsige Trump a kuma kawo karshen yin amfani da tsarin Wakilan zaben shugaban kasa, wanda tsarin mulkin Amurka ya tsayar a zaman hanyar zaben shugaba, wanda kuma ya sa Trump ya zamo shugaban kasa duk da cewa Hillary Clinton ta samu kuri’u fiye da shi a zaben.
A can yankin yammacin Amurka kuma, masu zanga zanga a biranen Los Angeles da San Francisco a jihar California, da birnin Portland a Jihar Oregon da kuma Seattle a Jihar Washington, sun yi maci suka tare hanyoyin mota domin nuna fusatarsu da samun nasarar Trump.
A yankin tsakiyar Amurka, an gudanar da zanga zanga a Chicago a Jihar Illinois, da tagwayen biranen Minneapolis-Saint paul a jihar Minnesota, da Omaha a Nebraska da kuma birnin Kansas bangaren Jihar Missouri.
Har a Jihar Texas ma wadda jiha ce ta ‘yan Republican, an gudanar da zanga zanga a wasu manyan biranenta ciki har da Dallas da Austin, babban birnin Jihar.
Babu dai wani rahoton tashin hankali a lokutan zanga zangar.
Babu wani daga bangaren Donald Trump da ya maida martani kan wadannan zanga-zangar nuna kyamar nasarar da ya samu da ake yi.