An dai gudanar da zanga-zanga a Portland, Oregon zuwa Chicago har New York a sassan daban-daban, yayin da wasu wuraren sunfi wasu yawan jama’a masu zanga-zangar musammam lokacin da aka tabbatar cewa Donald Trump ne ya lashe zaben a ranar Talata.
Shiko a sakon sa na Twitter a jiya Alhamis Trump yace da masu zanga-zangar wannan zaben shugaban kasa anyi shi cikin nasara, amma kuma kwararraru na shirya zanga-zanga wadanda kafofin yada labarai ne suka ingiza su, suna yin zanga-zanga, wannan bai dace ba.
Musali a Portland dubban masu zanga-zangar sunyi maci cikin birnin, abinda ‘yan sanda suka ce zanga-zangar ta rikide daga ta lumana ta koma ta fito na fito domin ko sun shiga farfasa tagogin shaguna suna kunna wutar da ake wasa da ita irin na bikin kirismeti ko sabuwar shekara.
Tuni ‘yan sanda suka ce wannan ba zanga-zangar lumana bace wannan yasa suke fadawa jamaa kar su tsaya wuri guda suci gaba da tafiya.
Jamiaan Sashen kula da sufuri na Oregon sun kulle hanyar sufuri ta tsakanin jiha da jiha mai lamba 5 da kuma mai lamba 84 domin gudun abinda ka iya faruwa mara dadi.
Amma a Denver masu zanga-zanga sun samu nasarar kulle hanya mai lamba 25 a daren jiya alhamis.