Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarar Trump Bata Yiwa 'Yan Nijar Dadi Ba


Masu zanga zangar kin jinin Donald Trump duk da zaben shugaban kasa da ya lashe da suka yi jiya a birnin New York
Masu zanga zangar kin jinin Donald Trump duk da zaben shugaban kasa da ya lashe da suka yi jiya a birnin New York

Kamar kasar Kamaru nasarar Donald Trump a zaben shugabancin kasar Amurka bata yiwa al'ummar kasar dadi ba saboda kyamar musulmi da ya keyi kamar yadda ya furta yayinda yake fafutikar neman zabe

A kasar ta Nijar jama'a na cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka na arba'in da biyar.

Wani Malam Isa ya fito karara yace basu ji dadin zaben na Trump ba saboda Hillary Clinton ta fi saukin lamari bisa Donald Trump. Yace duk wanda yake musulmi da mai kishin muslunci ba zai so abun da ya faru ba. Ya bayyana zai hana duk wani musulmi shiga Amurka. Hillary Clinton ta fi saukin lamari ta fi kuma sassauci ga musulmi da ma baki.

Kin zaben Hillary Clinton tamkar munafuncin amurkawa ne ya fito fili. Su ne suke zuwa Afirka su nunawa mutane babu banbanci tsakanin mace da namiji. Sun sha cewa lallai a dinga sa mata a harkokin siyasa a kasashen Afirka amma sai gashi su basu yi hakan ba. Ke nan mutanen Afirka suka rena. Sun gujewa akidar da suka cusawa Afirka.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

XS
SM
MD
LG