A wani lamari mai ban tausayi, iyayen dalibannan mata da aka sace a garin Cibok a makon jiya, sun shaida wa gwamnan jihar Borno, Honourable Kashim Shettima cewa adadin ‘ya’yan nasu da aka sace 234 ne, kuma 34 ne suka kubuta, sabanin rahotannin dake fitowa daga hukumomin makarantar na cewa adadin daliban 129 ne.