WASHINGTON, DC —
Sabon salo da kungiyar Boko Haram ta fito dashi kwanan nan inda take kai hari akan makarantu da kuma sace yara mata ya razana iyaye a jiharBorno.
Yanzu dai iyaye na cikin tsoro a jihar Borno domin barazanar da kungiyar Boko Haram take yiwa makarantun boko. Iyaye sun ce idan sun kai yara makaranta ana kashesu. Dalili ke nan da hankalin iyaye ya tashi.
Wani magidanci yace gaskiya basa kai yaransu makaranta domin suna tsoro domin kungiyar ta Boko Haram ta sha alwashin cigaba da kai hari akan makarantu.
Ba iyaye ne kadai ke jin tsoro ba. Malaman su ma suna cikin tsoro. Wani malami dake koyaswa a makarantar sakandare yace suna koyaswa ne amma ba tare da kwanciyar hankali ba. Yace lamarin zai shafi ilimi matuka. Yace suna bukatan addu'a.
Yanzu dai lamarin ya sa gwamnatin jihar Borno ta rufe makarantunta. Haka ma gwamnatin tarayya ta rufe makarantunta dake jihohin dake cikin dokar ta baci.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz