Yayin da gwamnan Borno ya kai ziyara a garin Cibok domin ya jajantawa iyayen da aka sace 'ya'yansu, iyayen su shaidawa gwamnan cewa yara 234 aka sace sabanin 129 da makarantar ta sha ambata.
Gwamnan jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako mai ritaya a wata wasika da ya aikawa kungiyar gwamnoni arewacin Najeriya, yace lallai akwai abin dubawa game da wasu abubuwan da suka faru cikin cikin kwanakinan.
Yayin da yake mayarda martani akan kiran da wasu suke yi cewa shugaba Jonathan ya nemi wani mataimaki daga arewa a madadin Namadi Sambo, Solomon Dalung yace a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa bai taimakawa arewa ba
Ganin yadda aka cigaba da yawan kashe-kashe cikin 'yan kwanakin nan kungiyar Izala ta koka da tabarbarewar tsaro a kasar Najeriya
Biyo bayan rikicin da ya barke a Ibi wanda yayi sanadiyar asarar rayuka mukaddashin gwamnan jihar ya kai ziyara yankin domin ya gani da idanunsa irin barnar da aka yi.
Gwamnan na Adamawa yace gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta kulla yakin kawar da 'yan arewa ta hanyar kisa, cin zarafi da yin ko oho da batun tsaron dake addabar yankin.
Mukaddashin gwamna Garba Umar ya ziyarci garin na Wukari yayin da jama'a ke kukar karancin abinci da ruwan sha a dalilin hana kowa fita
A yau 19 ga watan Afrilu ne za a cika shekara guda da kafa dokar-ta-bacin da mutanen Yobe suka ce bai tabuka komai a jiharsu wajen maido da tsaro ba.
Rundunar sojin Najeriya ta janye kalamun ikirarin da tayi na cewa wai ta kubutar da mafi yawancin ‘yan matannan, dalibai da aka sace su sama da 100 a cikin mokonnan, wadanda ake zaton ‘yan bindigan Boko Haram ne suka sace su.
Sarakuna na da daraja ta musamman da ake ganin kimarsu, kuma suna da rawar takawa dangane da tsaron al-ummomin Najeriya.
Sanadiyar mugun harin da 'yan ta'ada suka kan Nyanya shugaba Jonathan ya kira taron gaggawa da manyan jami'ansa.
Jihohin Adamawa da Yobe da Borno suke cikin dokar ta baci domin aika-aikar kungiyar Boko Haram to amma jihar Borno ita ce ta fi samun yawan hare-hare daga kungiyar. A kowane lokaci a ko ina kuma 'yan kungiyar su kan kai hari ba tare da an kamasu ba
Domin Kari