Yayin da ake kokarin ceto 'yan matan makarantar Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram ke rike dasu yau fiye da wata guda hukumar bada agajin gaggawa ko NEMA a takaice ta kai tallafin kayan abinci garin na Chibok
Gwamnatin Najeriya tace tana samun karbuwa a kasashen duniya duk da rikicin da Boko Haram ke haddasawa a kasar
Duk da yin watsi da dattawan jihar Borno suka yi da kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa akan daliban Chibok da aka sace, yanzu kwamitin din ya kai ziyara jihar ta Borno.
Maharan da suka kai hari sabon garin Kano sun ajiye motar ne sukayi tafiyarsu babu maharin a ciki
Taron Faransa wani sabon salo ne da turawan mulkin mallaka ke kokarin amfani dashi wajen ganin cewa sun rage katsalandan da suke yiwa kasashen da sukayiwa mulkin mallaka.
Senata Zanna ya bayyana fatar zuwan kasashen waje kan kokarin kubutarda 'yan mata 'yan makaranta zai kawo karshen rikicin.
Bayan da majalisar wakilai ta amince da karin wa'adin dokar ta baci yanzu jama'a sun sawa majalisar dattawa ido yayin da zata yi zamanta gobe.
Daren Lahadi wani bam ya tarwatse a Sabon Garin Kano wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar har da dan kunar bakin waken da ya tuka motar
Shugabannin Nigeria, Kamaru, Nijer, Chad da Benin sun halarci taro a Paris kan Boko Haram.
Wasu da ake jin ‘yan kungiyar Boko Haram na Nigeria ne sun tsallaka kan iyakarta da Kamaru, sun kai farmaki.
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya kuma ya fadawa taron Paris cewa yanzu Boko Haram tana gararamba a zaman al-Qa'idar Afirka ta Yamma
Rahotanni daga Waza mai tazarar kilomita 15 kacal daga bakin iyaka da Jihar Bornon Najeriya na cewa maharan su 200 sun kuma kashe wani sojan Kamaru guda daya.
Domin Kari