Babban makasudin wannan taro shi ne kyautata hadin kai wajen tsara dabarun tunkarar barazanar Boko Haram dake shiga da fita a tsakanin makwabtan
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya soke shirin zuwa garin Chibok.
Honorable Nuhu Zaki mai wakiltar Jihar Bauci a Majalisar Dokokin Najeriya, ya bada dalilan su na amincewa da tsawaita dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.
Kungiyar cigaban al'ummomin arewa ta tsakiya ta bukaci shugabannin addinin Musulunci da Kirista su hada kai da gwamnati a gano mutanen dake kiran kansu Boko Haram da masu mara masu baya.
Yayin da zake zantawa da wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu Shehun Borno Alhaji Garba El-Kanemi yace abun dake faruwa a jihar masifa ce.
Kungiyar mafarauta tana bukatar gwamnati ta janye sojoji daga dajin Sambisa kana su shiga su kakkabe 'yan kungiyar Boko Haram dake rike da 'yan matan Chibok.
Kamar ba za'a a yadda ba amma ba zato ba tsammani sai gashi majalisar wakilan Najeriya inda ak da shakka ta amince da sake sabunta dokar ta baci karo na uku a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.
Ganin gawarwakin 'yanuwansu sojoji da kungiyar Boko Haram ta hallaka yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga farautar yaran da kungiyar ta sace, wasu sun harzuka har ma sun yi harbe-harbe.
An yi kira ga 'yan boko haram dasu sako 'yan matan da suke garkuwa dasu.
Gamayya na kungiyoyin sa kai da na kwararru da kuma dalibai dake jihar kano sunyi gangami
Biyo bayan yadda majalisun tarayyar Najeriya suka ki amincewa da bukatar shugaban kasa kai tsaye ba tare da yin bincike ba abokiyar aiki Jummai Ali ta zanta da wani masani akan harkokin siyasa, tsaro da na yau da kullum dake koyaswa a jami'ar California Dr Baba Adam wanda shi ma daga jihar Borno ya fito.
Shugaba Jonathan ya sake mikawa majalisun tarayyar Najeriya karo na uku bukatar sabunta dokar ta baci a jihohin Adamawa, Borno da Adamawa to saidai sun ki amincewa kai tsaye ba tare da ji daga sifeton 'yansanda da hafsan hafsoshin sojoji da shugabannin jihohin da abun ya shafa ba.
Domin Kari