Wani marubuci kuma Malami,a sashen koyarda aikin jarida a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, Malam Kabiru Danladi Lawanti, yace taron na Faransa wani sabon salo ne da turawan mulkin mallaka suke kokarin amfani dashi wajen ganin cewa sun rage katsalandan da suke yiwa kasashen da sukayiwa mulkin mallaka.
Yace' maimakon ace inda wani rigima ya tashi a Nijer, ko a Najeriya ko a Kamaru ko a Chadi ace sun zo da sojojinsu sun kashe fitinar,yanzu abunda suke son yi shine su nuna cewa abunda zasu iya yiwa Afirka shine subada shawarwari da kuma wasu dabaru na leken asiri amma maganin matsalolin Afirka ita zata yi da kanta.
Malam, Kabiru Danladi Lawanti, ya kara da cewa abun kunya ne ga kasashen Afirka har sai Faransa ta kira su kafin su fara wannan abun, yaza ace kuna da matsala ku baza kuyi maganin taba zai wata kasa da take gefe,wanda kafin rikicin ya shafesu zai ya gama daku sanan ace sune zasu kira ku su gayamaku yanda za kuyi.
Yana mai kari da cewa akwai shuwagabanin wadanda yake suba shuwagabanin ne na damokradiya ba,kamar shugaban Kamaru da shugaban Chadi,kamar a Nijer zamu ce akwai damokradiya,sanan akwai son ci gaba wajen gudanar da harkokin mulki a kasashen Afirka.