A yayin da rundunar sojan Najeriya ta bakin kakakinta Janar Chris Olukolade take kara jaddada cewa manyan kwamandoji su na rike da rundunoninsu daram.
Askarawan sojin saman Najeriya sun kai hari a wasu yankunan da 'yan kungiyar Boko Haram suka mamaye a jihohin Adamawa, Borno da Yobe musamman ta wuraren Madagali.
Al'ummomin unguwar Wuntin Dada dake kusa da Bauchi jiya sun tashi cikin fargaba da tsoro sailin da wasu 'yanbindiga da kuma jami'an tsaro suka dinga harbe-harbe tsakaninsu har na tsawon mintuna arba'in.
Jiya aka cika kwana dari da talatin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a makarantar 'yan mata dake garin Chibok inda suka sace dalibai fiye da dari biyu wasu kuma suka tsallake rijiya da baya.
Rikici tsakanin kabilar Eggon da Fulani a jihar Nasarawa yanzu ya rikide ya koma na ramuwar gayya inda yanzu yayi sanadin rasa rayuka da kona gidaje.
Dubban 'yan gudun hijira suna kwarara zuwa garin Mubi dake arewacin jihar Adamawa lamarin da yanzu ya haddasa bullar cutar kwalara wadda ta kashe mutane da dama.
Gwabnatin Camaru tace sojojinta sun kashe wasu mutane guda talatin da ake zaton ‘yan Boko Haram, wanda akace sun afka inda sojojin Nigeria 480 suka tsallaka wajen fada da sojojin sa kan. Nigeria tace sojojin nata sun tsallakane alokacin da suke dubarun kare kai.
Manene hukumcin da sojojin zasu fuskanta
Kakakin sojojin Najeriya Chris Olu Kolade yace idan soja mai nuna bijirewa ne ko ya arce daga faggen daga ko ya nuna fargaba kiman sojan ta zube warwas.
A ranar lahadi nan da ta gabata ne wasu sojojin Najeriya, dauke da makamansu suka mika kansu ga sojojin kasar Kamaru.
Wani tsohon hafsan soja a Najeriya yace kin bin umurnin na gaba, babban laifi ne a kowace rundunar soja a fadin duniya...
Jama'ar karamar hukumar Madgali dake jihar Adamawa na zaman zullumi biyo bayan kawanyar da 'ayan kungiyar Boko Haram suka yiwa yankin tare da kafa tutotcinsu.
Domin Kari