Gwabnatin Camaru tace sojojinta sun kashe wasu mutane guda talatin da ake zaton ‘yan Boko Haram, wanda akace sun afka inda sojojin Nigeria 480 suka tsallaka wajen fada da sojojin sa kan. Nigeria tace sojojin nata sun tsallakane alokacin da suke dubarun kare kai.
Awani rahoton da gidan radiyon jahar Camaru ta rawaito tace sojojin kasar sun sha wahala ko rashin sa’a, a hari har biyu da ‘yan Boko Haram sukawo. ‘yan Boko haram din sunyi ta kokarin shiga kasar ta arewa inda tayi boda da jahar Borno, a shirye suke da kayan yaki. Alokacin harin na ranar talata sojoji sun kashe mutane goma sha daya kuma sun kashe goma sha shida a harin farko a akakai na ranar Litinin.
Sojojin na kasar Cameru sun kwacewa ‘yan Boko Haram din manyan makamai kuma sun lalata wata mota da suke amfani da ita.
Wannan hari yafarune a inda sojojin Nigeria suka tsallaka alokacin da suke fada da ‘yan boko haram din. Sojojin Nigeria, sunce sojojin su sun bada makamansu ga hukumar kasar Camaru, domin nuna musu babuwani abu a tsakanin kasashen biyu.
Bayan harin daya faru, awani rahoton gidan radiyo na kasar Camaru wanda yace shugaban kasar Paul Biya, ya bada izinin da a raka sojojin Nigeria bakin boda domin su koma kasarsu.
Shugaban kasar Biya yace “shugaban kasa yayi umarni da duk sojojin Nigerian da suka shigo masa kasa, da su zauna a gurin da aka basu kuma za’a sa sojojin Camaru da su ke kula dasu. Ambasu abinci, kula da lafiya, da kuma mai, kamar yadda shugaban kasar ya bada umarni. A lokaci guda kuma ana cikin shirin raka sojojin zuwa kasarsu.
Mai Magana da yawun bakin sojojin na Cameru wato Colonel Didier Badjeck, yagayawa muryar amurka cewa abinda gidan rediyon ya rawaitar, wannan ba tare da sanin su bane. Kuma muna kulawa sosai tunda sojojin Nigeriyar sunanan, saboda su ‘yan Boko Haram zasu iya zuwa da kayan sojojin Nigeriyar ko su kawo mana hari, to dole mu kula da wannan.
Yace kamata yayi mutane su goyi bayanmu su barwa sojojin Camaru su yaki ‘yan Boko Haram tunda su kwararrun sojojine.
Sudai 'yan Boko Haram an zarge sune da kame mutane, fada, da yin duk wani abu da yaketa doka.