Wani tsohon hafsan soja a Najeriya yace kin bin umurnin na gaba, babban laifi ne a kowace rundunar soja a fadin duniya, kuma irin wannan rashin ladabin ba al'ada ba ce a rundunar sojan Najeriya.
Birgediya-janar Idris Bello Dambazau mai ritaya, ya fadawa VOA a wata hira ta musamman cewa bin umurnin na gaba, shi ne ginshikin aikin soja, kuma shi yasa kowane soja yake daukar rantsuwar cewa zai bi umurnin na gaba da shi.
Tsohon hafsan yana yin furuci ne game da rahotannin dake cewa wasu sojojin Najeriya da aka tura bakin daga a Gwoza domin kwato shi daga hannun 'yan Boko Haram, sun ki tafiya su na kukar cewa ba a ba su makaman da suka dace domin gudanar da wannan aikin ba.
Yace lallai, hakki ne ga rundunar sojojin Najeriya ta samarwa da dakarunta kayan fadan da suka dace domin yakar 'yan ta'adda, kuma yana fata za a cika alkawarin da babban hafsan sojojin kasar yayi kwanakin baya cewa ana kan kokarin samar da kayan yaki masu inganci ga sojojin.
Baraka Bashir ce ta tattauna da shi.