Shugaban rundunar Sojan Najeriya, Kenneth Minimah ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai dake kula da harkokin sojin kasa, game da yadda aka kashe Nera Biliyan Daya da aka baiwa sojojin.
Mafarauta, 'yan tauri da jami'an tsaro sun hada karfi da karfe sun kwato kananan hukumomin Maiha da Mubi daga hannun 'yan Boko Haram.
Biyo bayan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a jihar Adamawa jama'a da dama suka fantsama zuwa wurare daban daban
Ganin yadda aka kwato kananan hukumomin Maiha da Mubi daga hannun 'yan ta'ada al'ummar Bama sun koka su ma a kwato masu yankinsu.
Kawo yanzu dai rahotanni daga arewacin jihar Adamawa na cewa ‘yan tauri, maharba da jami’an tsaro nafa cigaba da fafatawa da ‘yan bindiga na Boko Haram, kuma ma har an fara kwato wasu yankunan dake hannun ‘yan bindiga masu tada kayar bayan.
Mafarauta da 'yan tauri sun farma 'yan Boko Haram a jihar Adamawa sun kwato Maiha.
Inji Muhammed Haruna, cikin abun da ya kawo tabarbarewar tsaro shi ne wawure kudin da aka kebewa domin tsaro. Kudaden da yakamata a sayi makamai dasu a horas da sojoji duk an sacesu.
A jihar Adamawa yara 'yan firamare da shugabannin addinai suka tara sun yi addu'o'i da kuka wa Ubangiji domin ya kawar da masifar da 'yan Boko Haram suka jefa jihar ciki da wasu wuraren a Najeriya.
Jajantawar da ta'aziya da gwamnatin Najeriya tayi ya biyo bayan harin kunar bakin wake da wani dan ta'ada ya kai kan makarantar sakandaren gwamnati dake Potiskum wanda yayi sanadiyar mutuwar dalibai fiye da arba'in da biyar
Masu sha'awar tsayawa takara na amfani da hanyoyi daban-daban wajen jan hankalin 'yan jama'a yayinda ake shirin zabe mai zuwa.
Domin Kari