Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Najeriya Basu Damu da Abubuwan dake Faruwa Ba


Shugaba Jonathan
Shugaba Jonathan

Inji Muhammed Haruna, cikin abun da ya kawo tabarbarewar tsaro shi ne wawure kudin da aka kebewa domin tsaro. Kudaden da yakamata a sayi makamai dasu a horas da sojoji duk an sacesu.

Watakila su da suke shuganacin gwamnatin suna yin haka ne domin lamarin tabarbarewar tsaro suna ganin bai shafesu ba.

Idan yadda mahukunta suka fuskanci matsalar tsaron kasar ke nan rashin tunane ne mai zurfi, wato dai ya zama guntun tunane. Idan suna ganin abun bai shafesu ba ai akwai mutanen kudun a arewa. Misali Abuja yanzu ta zama tamkar wani birni a kudancin kasar. Idan suna ganin musulmai ne abun ya shafa watarana zai kai kansu.

Wakilin Muryar Amurka yace a ganin shi MuhaMMed Harauna babu yadda shugaba Jonathan zai ci zabe ba tare da arewa ba kuma abun mamaki akwai 'yan arewa da suke tare da Jonathan har suna cewa ya fi duk wani shugaba da kasar ta taba yi, to ko me ya kawo hakan?. Shin su 'yan arewan dake tare da Jonathan basu damu ba ne ko kuma mu ne bamu fahimci abun dake faruwa ba ne.

Muhammed Haruna yace a ganisa 'yan arewa dake tare da shugaban basu damu da abubuwan dake faruwa ba ne. Idan kuma ya damesu koda ba zasu bijire masa ba yakamata su nuna masa cewa wadannan abubuwan bai kamata ya amince dasu ba. Su nuna mashi cewa idan ba ya tashi yayi hobbasa ba babu yadda zasu iya sayar dashi ga arewa har ma su zabeshi.

Amma maimakon su yi hakan wasu da yawansu cewa suke tunda ake shugaba ba'a taba samun wanda ya yiwa Najeriya aika ba kamar Jonathan. Yace abun ban takaici ne a ce mutum mai hankali ya ce ba'a taba shugaba irin shi ba. Yace wannan ba batun addini ba ne. Abun kunya ne abun ban takaici.

Kwadayi ne yasa suke daukan wannan matsayin. Mutane wadanda basu da wadatar zuci. Abun da suka tara har tattaba kunnensu zasu gada amma bai ishesu ba saboda haka kullum tunanensu abun da zasu samu da 'ya'yansu da abokanansu ya damesu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG