Biyo bayan labarin cewa an kwato Maiha da Mubi dukansu a jihar Adamawa daga 'yan kungiyar Boko Haram, Muryar Amurka ta zanta da babban jami'in fadar gwamnan jihar Adamawa Malam Chubado Babbi Tijjani.
Malam Tijjani ya tabbatar da kwato yankunan a firar da yayi da Muryar Amurka. Yace kowa ya san halin rashin tsaro da arewa maso gabashin kasar ta shiga. To amma da yaddar Allah sojojin Najeriya da mafarauta da wasu sun kwato wuraren biyu. Yace musulmai da kiristoci sun hadu suna ta yin addu'o'i Allah ya kawo karshen bala'in da ya addabi kasar musamman jihar. Yanzu garin Maiha da Mubi sun shiga hannun gwamnati.
Dangane da rahoton cewa an samu hargitsi a Hong da kuma Gombi Malam Tijjani yace yanayin da ake ciki yanzu ko da allura ce ta fadi mutane zasu firgita. Ko mace ce tayi tuntube ko yaro ya gudu mutane zasu kama gudu sabili da tsoro ya riga ya shiga zukatan mutane.
Halin da ake ciki yanzu ba'a iya banbantawa tsakanin 'yan Boko Haram da barayi da sauran mugayen mutane. Idan barawo yana son firgita mutane sai ya ce shi Boko Haram ne. Abubuwa dai sun tabarbare. Malam Tijjani ya tabbatar an yi harbe-harbe a Gombi da Hong amma komi ya lafa mutanen da ake zargin cewa 'yan ta'ada ne sun bar jihar zuwa jihar Borno.
Ga karin bayani.