Ana nan ana tafka muhawara a Majalisar Dattawan Nijeriya kan bukatar Shugaba Goodluck Jonathan ta sake kafa dokar ta baci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. A gobe ake sa ran su ma 'yan Majalisar Wakilai za su shiga tattaunawa a kai.
Kiran da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu yayi, na cewa al-umma su tashi, su kare kawunansu, yana samun goyon bayan jama’a.
Daya daga cikin ‘yan majalisar dattawa a Najeriya daga Jihar Borno, Sanata Muhammed Ali Ndume yace baya goyon bayan shirin da gwamnatin Najeriya take yi na sabonta dokar ta baci a Jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
Yayin da gwamnatin tarayya ke sabunta dokar ta baci a Borno, Yobe da Adamawa, karo na uku da ake sabunta dokar tsohon gwamnan jihar yace kasancewa cikin gwamnatin tarayya ne kadai zai kawo karshen fitinun.
Hadakar kungiyoyin maharba ko mafarauta da 'yan kato da gora ko 'Civilian JTF' sun karyata rahoton da ke cewa an kama shugabanninsu.
Cikar wa'adin dokar tabaci a karo na uku da ake kafa a yankin arewa maso gabashin.
Ban din da wata 'yar kunar bakin wake ta tarwatsa ya hallaka mutane 12 tare da ita
Matasan garin Azare sun aika da wasu mutane biyu lahira da ake zargi su ne suka kai hare-hare a garin.
Kakakin gwannatin jihar Mr. Peter Elisha yace maimakon haka gwamnatin tana shirin kara tallafawa irin wadannan matsa.
Gwamnan wanda yake magana a hira da Muriyar Amurka yace matsalar tsaro al'amari ne d a ya buwayi duniya baki daya yau, ba Najeriya kadai ba.
A makon jiya ne mayakan sakan na kungiyar Boko Harama suka kama garin na Chibok inda su kwashi 'yan mata fiyeda metan a farkon shekaran nan.
'Yan kato da gora da kuma mafarauta ne da suka sami goyon bayan jami'an tsaro suka kwato garuruwan Mubi da kuma Maiha.
Domin Kari