Wata 'yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a wata kasuwa a arewa maso gabashin Nijeriya, ta hallaka mutane akalla 12.
Nan take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin na jiya Lahadi a Azare, wani gari a jihar Bauchin Nijeriya, to amma a baya kungiyar Boko Haram mai tsattsauran ra'ayi ta kai hare-hare makamantan wannan, a fafatawar da ta ke yi da gwamnatin kasar.
Tun da safiyar jiya Lahadin, sojojin Nijeriya sun ce sun fatattaki 'yan Boko Haram daga garin Chibok na arewa maso gabashin Nijeriya, garin da su ka sace 'yan mata dalibai sama da 200 a farkon wannan shekarar.
Jami'an sojin sun ce sun sake kwato garin ne, a wani matakin sojin da su ka dauka da yammacin ranar Asabar, kwanaki biyu kawai da kwace garin da Boko Haram ta yi.
Mutanen garin sun ce sojojin sun sami taimako daga 'yan banga.
Babu wani bayani game da adadin wadanda arangamar ta jiya Lahadi ta rutsa da su.