Cikar wa'adin dokar tabaci a karo na uku da ake kafa a yankin arewa maso gabashin, Najeriya,da alamu, wasu jama’ar yankin na ganin cewa duk da kafa dokar tabaci, kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
Ko da yake hadin gwiwar da aka samu tsakani Sojoji, da kato da gora wato Civilian JTF, da kuma kungiyoyin maharba, zai taimaka, gaya wajen yakin da ake yi da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, ya samu goyon bayan jama'a, da dama inda wasu ke masu shawaran cewa ya kamata a samarwa ‘yan kato da gora da maharba, makamai, na zamani, domin yakin na yanzu na zamani ne.
Yanzu kuma, Jama’ar yankin sai ce-ce-ku-ce, suke yi dagane da batun cire Gwamnonin yankin, da aka kafawa dokar tabaci, batun da Danjuma Musa, wani manazarcin siyasa ke cewa wannan ba shine mafutaba, yace abun yi shine Sojojin mu su kasance masu fada da kishin kasa, kuma su sami kyakkyawan hadin kai.