Zaman lafiyar Taraba ya fi muhimmancin da duk wani abun da zai kawo tashin hankali inji Tsohon kakakin majalisar jihar.
Kungiyar Jama'atul Nasril Islam ta fito fili tace akwai bukatar 'yan Najeriya su kare kansu daga hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.
Wasu wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane ashirin da biyar a garin Doron Baga, a arewa maso gabashin Nigeria.
Gwamnatin jihar Borno ta fito da wani shirin rabawa marasa galifu abinci kyauta a fadin birnin jihar domin rage radadin talauci da halin kuncin da suka shiga.
Hotunan hayaniya a harabar majalisar dokokin Najeriya yau Alhamis, lokacinda jami’an tsaro suka hana kakakin majalisa Aminu Tambuwal shiga.
Bayanai da rundunar tsaron kasa ta bayar tace ana samun nasara wajen tusa keyar 'yan binidgar.
Hakan ya biyo bayan yunkurin da jami'an tsaro suka yi na hana kakakin majalisar Aminu Waziri Tambuwal, shiga cikin zauren majalisa.
Wasu na ganin cewa kasawar gwamnati, kasawa ce ta 'yan arewan dake kan mukaman kula da tsaro
Kungiyar Arewa Citizen Action for Change ta ce 'yan majalisar dokokin Najeriya su yi tunani
A yau ma majalisar dattijan tayi zamanta ne cikin sirri, kuma wakilan sunki suyi magana bayan da suka fito.
Ganin yadda mafarauta su ka fatattaki 'yan Boko Haram daga garuruwan Mubi da Maiha da sauran wurare a arewa maso gabashin Nijeriya, jama'a na cigaba da jinjina masu.
Allah ya ba wasu mata a Gombe sa'ar hallaka wani dan kunar bakin wake tun kafin ya sami aikata aika-aikarsa.
Domin Kari