Yanzu haka dai an bude wani sabon shafi a danbarwar siyasar jihar Taraba, lamarin da ya sa kakakin majalisar jihar Josiah Sabe Kente yin murabus daga mukaminsa. Ba tare da bata lokaci ba aka nada Honarable Mark Hussain ya maye gurbinsa. Haka kuma nan take suka kada kuri’ar amincewar da mataimakin Gwamnan jihar wanda kotun koli ta maido a makon jiya wato Alhaji Sani Abubakar Danladi a matsayin sabon Mukaddashin Gwamnan jihar.
Tsohon kakakin majalisar jihar Honarable Josiah Sabe Kente, dake da alaka ta ku-da-kud da tsohon Mukaddashin Gwamnan jihar Alhaji Garba Ummar wato UTC, ya fadi cewa ya ajiye mukaminsa ne ba don komai basai don samun zaman lafiya a jihar. biyo bayan labarin da Honarable Kente ya samu cewa an ba ‘yan sanda umurni su hana shi shiga majalisar kuma za a tsige shi.
Haka kuma ‘yan bangaren tsohon Mukaddashin Gwamnan jihar da jam’iyyar PDP ta tantance don yi mata takara a zaben da za a yi ‘yan makonni masu zuwa, wato Alhaj Ummar UTC sun bukaci magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu. Injiniya Yusuf Gamaliya, darektan kemfe din UTC, yace duk da abin da ke faruwa a jihar, su fa basu razana ba, kuma suna nan daram.
Yanzu dai an zuba ido ne a ga yadda wannan sabuwar danbarwa zata kaya, inda ko wane bangare ke ikirarin shi ke da jama’a.
Kamar yadda za ku ji a nan, ga wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz da karin bayani.