Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa a Gombe Sun Hallaka Wani Dan Kunar Bakin Wake


Matasa da mafarauta da sauran jama'ar gari na kara taimakawa wajen tabbatar da tsaro a arewa maso gabashin Nijeriya.
Matasa da mafarauta da sauran jama'ar gari na kara taimakawa wajen tabbatar da tsaro a arewa maso gabashin Nijeriya.

Allah ya ba wasu mata a Gombe sa'ar hallaka wani dan kunar bakin wake tun kafin ya sami aikata aika-aikarsa.

Wani dan kunar bakin wake, wanda ya shirya yin mummunar barna, ya gamu da ajalinsa ba tare da ya cimma burinsa ba. Wannan kuwa ya biyo bayan dago shi da wasu matasa su ka yi a wata tashar motar Gombe, babban birnin jihar Gombe.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Gombe Abdullahi Kudu ya ce tare da taimakon ‘yan unguwa da kan taimaka masu, Allah ya ba su sa’ar bankado aniyar wannan dan kunar bakin waken. Ya ce sun yi sa’ar kwance wasu muggan bama-baman da idan ba don Allah ya kare ba da sun yi sanadin mutuwar mutane da dama. Yace sun sami gurneti biyar da kwansan bam biyu silinda biyu da kuma kunamu biyar.

Wakilinmu Abdulwahab Muhammad, wanda ya tura da rahoton ya ce matasan da ke Tashar Motar Gombe Line, sun shiga dibgarsa ne bayan da su ka lura cewa ya na yinkurin tayar da bam din ne. Shi kuwa wani ganau, wanda ya kira Abdulwahab yayin da aka jefa tayu kan gawar dan kunar waken ana Konawa, ya tabbatar cewa sai da aka tabbata cewa ya na da bakar aniya aka hallaka shi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG