Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula sun zamo ruwan dare a yankin arewa maso gabashin Najeriya a dalilin hare-haren ‘yan Boko Haram. A yayin da wannan tashin hankali ke bazuwa zuwa wasu sassan na Najeriya, har ma da makwabtanta, fargaba tana kara yawaita cewa watakila gwamnatin Najeriya ba ta san yadda zata takali wannan batu ba. Ko kuma tana kara rura wutar fitinar ne ma da kanta.
‘Yan kato da gora, da mafarauta na amfani da bindigogin gargajiya wajen zirga-zirga domin kare garuruwansu daga hare-haren Boko Haram.
Rundunar sojojin kasar Kamaru tace dakarunta sun kasha mayakan Najeriya 116 daga wata kungiyar Boko Haram a arewacin kasar, Disamba 18, 2014.
Wasu sojojin Najeriya da aka yanke ma hukuncin kisa.
‘Yan kungiyar Boko Haram, Sun dade suna musgunawa jama’ar, arewacin Najeriya.
Kwararru sun bayyana tababa a kan ko matan da ake amfani da su wajen kai hare-hare 'yan kunar-bakin-wake ne ko wani abin ne dabam.
Shugaba Jonathan na Najeriya ya sha yin alkawarin murkushe kungiyar Boko Haram amma maimakon hakan kungiyar sai dada fadada ta'adanci ta keyi tare da hallaka rayuka da dukiyoyi
Rundunar tsaro ta Jos jihar Filato ta tabbatar da tashin bama-bamai da kuma asarar rayuka.
Kwana daya da harin kunar bakin wake do bom a birnin Kano, wasu boma-bomai sun fashe a kusa da babbar kasuwar Taminus dake Jos.
Domin Kari