Kwararru a fannin tsaro a Najeriya sun bayyana cewa da alamun matan da ake amfani da su wajen kai hare-haren bam na kunar-bakin-wake, ba wadanda suka shiga wannan abin da son ransu ba ne, watakila anyi amfani da wani abu aka juya musu kwakwalwa, ko kuma dai tayar da bam din da aka rataya musu ake yi daga can nesa.
Wani kwararre kan harkokin tsaron da yayi magana da VOA Hausa, yace da alamun matan da ake amfani da su din, wadanda ba su da hikimar da zasu iya kare kawunansu daga shiga irin wannan lamarin ne, kuma, ana yi musu sihiri ne.
Yace ana ba su wani abu na sihirin da su na yin amfani da shi sai su ji babu abinda suke sha'awa kamar aikata kisan, yana mai cewa "na shaida hakan a Sierra Leone, an yi amfani da irin wadannan yara aka ba su magani. Wadanda muka kama, a bayan da wannan maganin ya bar jikinsu sun ce ana (ba su magunguna) masu yawan gaske dake fitar da su daga hayacinsu ne."
Yace da aka ba su sai suka ji babu abinda suke son yi illa suyi ta yanke hannu ko sarar mutane.
Yace babu abinda ya bambanta irin abinda ya gani a kasar Sierra Leone da abinda yake faruwa yanzu haka a Najeriya.
HANYOYIN GANE MASU DAUKE DA BAM A JIKINSU
Kwararren yace babban abin lura shi ne zai yiwu a gane mutum mai dauke da wani mummunan abu a jikinsa, ciki har da yawan gumi, yadda za a ga mutum yana ta zuba gumi, koda ba lokacin zafi ba a saboda yadda gabansa ke faduwa.
Haka kuma yace zai yiwu a ji warin wani turaren da aka yi wa mai dauke da bam din kafin ya fito, ko turaren da ya shafa na boye warin abinda yake dauke da shi.
Za a ga idanun mutum yayi Ja-Zur, ko a ga alamun akwai wani abu a kumshe a jikinsa. a saboda yadda yake tafiya.
Yace idan an ga wadannan alamun, kada a tinkari mutum, a kira lambobin jami'an tsaro da aka yi ta rarrabawa, domin kusantar irin wadannan mutane na da matukar hatsari.
Ga cikakken bayani...