Shugaban yayi alkawarin murkushe ta'adanci duk da abun da ya bayyana a zaman yunkurin da wasu keyi na sa kafar angulu ga kokarin murkushe 'yan kungiyar Boko Haram.
Duk da matsalar Boko Haram da shugaban bai shawo kanta ba har yanzu, jam'iyyar PDP ta sake tsayar dashi a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za'a yi badi.
Masu caccakar manufofin gwamnatin Najeriya sun ce shugaba Jonathan bai cancanci samun wani karin wa'adin mulki ba domin gwmanatinsa ta kasa kawo karshen ta'adanci da kungiyar Boko Haram ta haddasa a kasar. Haka kuma masu caccakarsa sun ce shugaban ya kasa kare 'yan Najeriya daga hare-haren 'yan Boko Haram. Haka kuma sun zargi gwamnatinsa da kasa iya gudanar da harkokin mulki yadda ya kamata. Shugaban ya kuma kasa farfado da tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al'ummar kasar.
Mai magana da yawun shugaban Reuben Albati yayi watsi da caccakar akan cewa siyasa ce kurum. Yace masu hamayya da shugaba Jonathan suna anfani da matsalar tsaro domin biyan bukatunsu a siyasance sabili da zaben da za'a yi badi.
Reuben Albati ya cigaba da cewa shugaba Jonathan ya sha fada cewa karfin jama'a da na gwamnati a hade sun fi karfin 'yan ta'ada da 'yan tawaye. Shugaban ya lashi takobin daukan duk matakan da suka zama dole. Komi dadewa gwamnati ta kuduri aniyar murkushe 'yan Boko Haram. Sabili da neman zabe mutane da dama suna siyasa da yaki da tarzoma. Shugaban ya ce kalubalen da ake fuskanta yana bukatar hadin kan duk 'yan Najeriya da kuma tunkararsa ba tare da banbancin siyasa ba.
Ga Jummai Ali da karin bayani.