Sojojin Najeriya na cigaba da farautar mayakan sa kan boko haram a dajin Sambisa da sauran wurare, tare da ceto wasu da 'yan kungiyar suka yi garkuwa da su.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin adadin rayukan da suka salwanta a lokacin rikin garin Zariya tsakanin sojojin Najeriya da mabiya Mazahabar Shi'a.
A jiya Lahadi ne rikicin da ya kunno kai tsakanin mabiya Shi’a da sojojin Nijeriya a ranar Asabar ya ci gaba har ya haifar da kame shugabansu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky da kashe wasu daga cikin mabiyansa da masu tsaron lafiyarsa da ma babban likitansu da kuma kakakin shi El-Zakzakin.
Jami'an 'yan sanda sun tsaya kusa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja, domin kula da kara tabbatar da tsaro.
Jakada Amurka Michael Hoza, ne ya mikawa Ministan tsaron kasar Kamaru.
Rahotanni daga janhuriyar Nijar sun bayyana cewa hukumomin kasar na kokarin mika wasu ‘yan boko haram ga hukumomin Najeriya bayan da aka shafe lokaci mai tsawo ana tsare da su a gidajen yari daban daban.
A farkon wannan shekara shugaba Muhammdu Buhari na Nigeria,ya baiwa rundunar sojan Nigeria wa'adin watan Disamba na murkushe yan kungiyar Boko Haram.
Kungiyar masu rajin kare hakkin bi'adam a Najeriya sunyi kira da gwamnatoci su inganta rayuwar mazauna sansanin 'yan gudun hijira a kasar baki daya.
Kasar Kamaru ta sanar da cewa rundunar sojojinta sun kashe ‘yan boko haram guda 100 tare da tserar da mutane kimanin 900 da su ‘yan ta’addar masu mazauni a Najeriya suka yi garkuwa da su.
A wani gefen kuma, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce adadin wadanda aka kashe a wannan harin ya karu zuwa mutum 34.
Karin matakan tsaro, musamman a yankunan da suke bakin iyaka da Najeriya, na zuwa yayin da Kamaru ta ke jiran isar sojojin taron dangi na Afirka wadanda zasu hadu su murkushe sauran mayakan Boko Haram
Domin Kari