A wani gefen kuma, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce adadin wadanda aka kashe a wannan harin ya karu zuwa mutum 34.
Karin matakan tsaro, musamman a yankunan da suke bakin iyaka da Najeriya, na zuwa yayin da Kamaru ta ke jiran isar sojojin taron dangi na Afirka wadanda zasu hadu su murkushe sauran mayakan Boko Haram
Hotunan wasu mata da yara da Sojojin Najeriya suka ceto daga dajin Sambisa dake arewa maso gabashin Najeriya.
Tun bayan da Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya, dubban mutane ne suka rasa rayukansu kana wasu miliyoyi suka fice daga muhallansu.
‘Yan Najeriya da suke cikin wahalar shekaru shida na rikicin yakin ‘yan Boko Haram da rundunar sojojin kasar, sun fara samun taimako daga kungiyoyin agaji na duniya.
Sojoji dake jihar Adamawa a kauyen Kubula sun cafke wata dake kokarin kai harin kunar bakin wake.
Rundunar mayakan sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane goma sha hudu da kuma wasu ashirin da tara da suka sami raunuka, sakamakon tashin boma bomai da ya auku a cikin garin Maiduguri.
Bayanai daga Jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa ana samun karuwar yawan mutanen da suka mutu a hare-haren bam da aka kai a birnin Maiduguri.
A daidai lokacin da sojoji ke ikirarin samun galaba kan 'yan kungiyar Boko Haram a yakin da su keyi sai gashi 'yan ta'adan na kara yawan tada bamabamai cikin Maiduguri da kewaye
Biyo bayan bam da ya tashi a sansanin 'yan gudun hijira a Yola jihar Adamawa shugaban Najeriya ya bada umurnin karfafa tsaro a sansanin.
Rikicin kailanci da na addini na neman zama ruwan dare gama gari a jihar Taraba inda wasu sun yaudari wasu shugabanin al'umm daga bisani suka hallakasu.
Domin Kari