Wasu masu tsare-tsaren agaji su biyu sun kuduri aniyar agazawa kananan yaran da rikici ya farrakasu da maganar karatunsu, sai kuma matan da rikicin ya maida zawarawa.
Shiri daya zai yi aiki a makarantun wucin gadi sama da 300 a jihohin Bauchi da Gombe da Adamawa don ci gaba da karantar da yaran da rikicin Boko Haram ya raba da karatu.
Wata kungiya mai zaman kanta ce anan Washington mai suna Creative Associates International zata jagoranci aikin tare da tallafin kudi daga hukumar Amurka ta raya kasashe masu tasowa wato USAID.
Ayyukan zasu dogara ne da tallafin shugabannin al’umman kasar don bada gudunmawa a wuraren da ke da tsaro don gudanar da koyarwa. Kamar yadda daraktar ilimin yankuna masu rikici ta kungiyar Eileen St. George ta bayyana.
Kimanin yara Miliyan daya ne rikicin Boko Haram ya raba da hanyar samun ilimi a dalilin hare-haren ta’addanci a yankunan, kamar yadda kungiyar mai zaman kanta ta bayyana.