Alkali mai kare muradun hukuma (Procureur de la Republique) ya gargadi ‘yan siyasa a Jamhuriyar Nijar su daina amfani da kalaman kabilanci a yakin zaben dake gudana a yanzu haka.
Kungiyar Cinikayya ta Duniya ta fitar da wani faifan bidiyo da nufin gabatar da sabuwar shugabar da aka zaba yau.
An cigaba da kara samun riga kafin annobar coronavirus.
Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) ta tabbatar da zaben tsohuwar minister kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar, da kawo karshen jan kafa da aka yin a tsawon watanni a cike gurbin babban darektan kungiyar da ke da shalkwata a Geneva.
Hukumar dake sa ido kan kafafen labarai a China, ta ce ta dakatar da kafar labaran BBC daga gudanar da ayyukanta a kasar, saboda abin da ta kira “Saba ka’ida sosai game da batutuwan yadawa a labarai.”
A yau Talata kasar Peru ta fara yaki da annobar coronavirus ta biyu da ta sake kunno kai, inda shugaban kasar Francisco Sagasti ya bayyana cewa allurar rigakafin bata da illa.
Hukumomi sun ci gaba da tsare Jimmy Lai, wani hamshakin dan kasuwa mai harkokin sadarwa kuma dan rajin dimokaradiya a Hong Kongbayan da babbar kotun yanki ta hana bada belinshi yayin da ya bayyana gaban ta yau Talata.
An gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin sojan Myanmar a rana ta uku a jere, yau Litinin, mako guda bayan da sojoji suka tsare Aung San Suu Kyi, da sauran shugabannin zababbiyar gwamnatin farar hula.
Hukumomi a Haiti sun ce sun dakile wani yunkurin da aka yin a kashe shugaba Jovenel Moise tare da kifar da gwamnatinsa a jiya Lahadi, yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan yaushe wa’adin mulkinsa zai kare.
Dubban mutane sun fito a fadin Myanmar a yau Lahadi domin bayyana rashin amincewar su ga juyin mulkin makon jiya da kuma neman sakin zababbiyar shugaba Aung Sang Suu Kyi, a wata zanga zanagr da ba a taba ganin ba tun bayan juyin juya hali a shekarar 2007 da ya taimakawa sauyin dimokaradiyar kasar.
Tsohuwar minister kudi ta Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala tana kan hanyar zama darektar hukumar cinikayya ta duniya inda idan aka zabe ta, za ta zama mace da farko kuma bakar fata ta farko da zata rike wannan mukamin a tarihin kungiyar cikin shekaru 25 da kafa ta.
Sakamakon wani bincike da Jami’ar Oxford ta fitar yau Laraba ya nuna cewa maganin rigakafin korona birus da kamfanonin AstraZeneca da Jami’ar ta Oxford suka samar, yana rage yaduwar kwayar cutar da kashi biyu bisa uku.
Domin Kari