Dubun-dubatar mutane sun toshe titunan manyan biranen Myanmar da yawa, ciki har da Nay-pyi-taw, babban birnin kasar, da kuma babban birnin kasuwanci na Yangon, suna rike da alamun da ke cewa "A ceci Myanmar" "Muna son dimokiradiyya," da kuma hotunan Suu Kyi.
‘Yan sanda sun yi amfani da mesar ruwa don tarwatsa masu zanga-zangar a Nay-pyi-taw.
Zanga-zangar ta shiga wani sabon salo yau Litinin yayin da ma’aikatan gwamnati, da ma’aikatan jirgin kasa, da malamai da ma ma’aikata a wasu sassan suka fara yajin aiki a duk fadin kasar.
An sake dawo da hanyar sadarwar Intanet a jiya Lahadi, kwana guda bayan an katse shi, wanda hakan ya bai wa 'yan kasar damar yayata zanga zangar kai tsaye, tare da sanya bidiyo a shafukan sada zumunta, na zanga-zanga daban-daban da ke gudana a fadin Myanmar.