A wata sanarwar da aka rarrabawa kafafen yada labarai mai dauke da sa hannun babban alkali mai kare muradun hukuma Procueur de la Republique a kotun birnin Yamai, mai shara’a Maman Sayabou Issa yace yana bin diddigin abubuwan dake faruwa a yakin neman zaben da ke gudana a yanzu haka saboda haka ya tunatar da ‘yan siyasa da ‘yan farar hula da dukkan ‘yan kasa cewa kundin hukunta masu laifika ya tanadi hukuncin zaman kason shekaru 5 tare da haramcin zama a kasar Nijer ga duk wanda aka kama da laifin nuna dabi’un kabilanci ko nuna bambancin launin fata da jihanci ko tauye hakkin yin addini da nufin haddasa fitina a tsakanin jama’a.
Sanarwar ofishin alkalin ta kara da cewa aya ta 171 ta kundin hukunta laifika ta tanadi tarar jakka 50 (50000) zuwa 500 na cfa (500.000) ga duk wanda ya soki hukuncin kotu ta hanyar rubutu kokuma a bayyane.
Duk da yake a dunkule aka yi wannan tunatarwa wasu na ganin daga yanzu za a ci gaba da cece kuce akan halaccin takarar Bazoum Mohamed da ake zargi da mallakar jabun takardar shaidar zaman dan kasa tamkar wani fito na fito ne da hukuma.
Da ma dai a jijibirin fitar da wannan sanarwa kungiyar farar hula ta CADDRH ta bukaci tsohon Firai Minista Hama Amadou ya roki gafara a wajen ‘yan Nijer saboda zarginsa da furta kalaman kabilanci a yayin wani taron gangami dan takarar ‘yan adawa a makon jiya a birnin Yamai .
Sai dai wani jigo a jam’iyar Moden Lumana ta Hama Amadou wato Alhaji Lawali Salissou mai lakanin leger yace an yiwa kalaman tsohon Firai Ministan mumunar fahimta ne.
A ranar 21 ga watan fabrerun ne talakawa million 7.da kusan dubu 500 da suka yi rajista zasu raba gardama a tsakanin dan takarar ‘yan adawa Mahaman Ousman mai fafitikar samar da canji da na bangaren masu mulki Bazoum Mohamed dake fatan ci gaba da ayyukan da shugaba Issouhou ya gudanar a tsawon shekaru 10 da ya yi akan karagar mulki.
Saurara cikakken rahoton Souley Moumini Barma a Sauti: