Kungiyar ta sanar da zaben tsohuwar Ministar kudin ta Najeriya a shafinta na twitter inda ta ce "an zabi Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya a matsayin sabuwar Darekta- Janar ta WTO. Dr. Okonjo-Iweala ta yi tarihi a matsayin mace ta farko kuma 'yar Afrika ta farko da za ta shugabanci WTO. Za ta fara wa'adin shugabancinta ranar 1 ga watan Maris 2021."
Tun farko Kungiyar WTO ta wallafa a shafinta na twitter cewa, yau zata zabi Idan aka zabe ta, matsayin shugabar kungiyar, za ta kasance mace ta farko kuma ‘yar asalin Afrika ta farko da ta rike matsayin shugabar kungiyar.
Ngozi Okonjo-Iweala ta gaji Roberto Azevedo dan asalin kasar Brazil wanda ya sanar a watan Mayu cewa, zai sauka daga mukamin kafin cikar wa’adin aikinsa ya kuma bar kujerar shugabancin kungiyar a farkon watan Agusta.
Hukumar ta dauki lokaci mai tsawo tana kokarin zaben sabon shugaba daga jerin wadanda suka tsaya takara da suka hada da mata da dama kafin daga baya takarar ta fi karfi tsakanin mata biyu, Yoo Myung-hee, minister harkokin cinikayya ta kasar Koriya ta Kudu mai ci yanzu, da kuma tsohuwar ministar kudi ta Najeriya kuma tsohuwar darekta a babban bankin duniya, Ngozi Okonjo-Iweala.
Kungiyar ta kasa cimma matsaya kan wanda za a zaba tsakanin ‘yan takarar mata biyu sabili da taka birki da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wanda ya nuna rashin goyon bayan fitattun ‘yan takarar. Sanarwar da Yoo Myung-hee, ta yi na janyewa daga takarar makon jiya, da kuma goyon bayan takarar Ngozi Okonjo-Iweala da gwamnatin shugaba Joe Biden ta nuna ya share fage ga Dr, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama shugabar kungiyar.
Tuni Dr Ngozi Okonjo-Iweala ta zayyana matakan da zata dauka nada tunkarar kalubale da kungiyar ke fuskanta da nufin ganin ta cimma manufa da kuma farfado da kungiyar yadda za ta yi tasiri a harkokin cinikayya da ya kasance manufar kafa kungiyar, da kuma shawo kan matsaloli da suka addabi kasashen duniya da suka hada da yaki da cutar Coronavirus.
ngozi-okonjo-iweala-tana-kusantar-zama-shugabar-wto
wto-dalilin-da-ya-sa-amurka-ba-ta-goyon-bayan-ngozi-okonjo-iweala
takarar-ngozi-okonjo-iweala-buhari-zai-shiga-kamfe
Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.