Gwamnatin Birtaniya ta kulla yarjejeniya da kasar Rwanda domin aikewa da wasu masu neman mafaka zuwa kasar dake gabashin Afirka, matakin da 'yan siyasa masu adawa da 'yan gudun hijira suka yi Allah wadai da shi.
A yayin da aka shafe fiye da wata daya ana yaki tsakanin Rasha da Ukraine, kasashen duniya daban daban na ci gaba da bayyana tasirin wannan yaki ga tattalin arzikinsu.
Yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin sojojin Rasha da Ukraine, sannu a hankali yakin na yin tasiri sosai a fadin duniya, musamman ma ta fuskar tattalin arziki, wanda ke shafar farashi da kuma batun samar da wasu kayayyaki a kasuwannin duniya.
A cikin watan Maris, lokacin da Shugaba Joe Biden ya yi sanarwar maraba da 'yan gudun hijirar Ukraine 100,000, inda ya ba da matsayin kariya na wucin gadi ga wasu 30,000 da suke zama a Amurka tare da dakatar da hana korar 'yan kasar Ukraine.
Matasan bakar fatar Afurka suna kaurin suna wurin aikata kaifuka a birnin New York a cewar jami’an tsaron birnin.
Albright ta rasu ne bayan fama da cutar kansa kamar yadda iyalanta suka sanar a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
Kasar Rasha ta bai wa kasar Ukraine wa’adin zuwa safiyar yau Litinin ta mika birnin Mariupol da Rasha din ta mamaye, yayin da Shugaban Ukraine Volodymyrr Zelenskyy ya ce a shirye yake don tattaunawa tare da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin.
Jami’an Amurka sun ce mummunan harin da Rasha ta kai bangaren yammacin kasar Ukraine jiya Lahadi, kusa da kan iyaka da Poland, wani abu ne da suka yi tsammani.
Dole ne duniya ta rika tunawa da halin da wadanda ke rayuwa cikin yakin da aka kwashe shekaru ana gwabzawa a Yemen su ke ciki, in ji wata jami'ar kungiyar agaji ta Red Cross a jiya Juma'a.
Tracy Eboigbodin, 'yar shekara 28 daga Verona 'yar Najeriya, ta lashe gasar girkin MasterChef Italia karo na 11.
Hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta Rasha ta hana shiga gidajen yanar gizo na kafofin labaran kasashen waje da dama da suka hada da BBC da Deutsche Welle saboda yada abin da ta ayyana a matsayin labaran karya, a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan rahotanni kan Ukraine.
Darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta nema Alhaji Bashir Garga yace yan Najeriya 450 ne suka dawo gida Najeriya ta filin jiragen sama na Abuja.
Domin Kari