“Wannan bai zo wa jami’an leken asirin Amurka da jami’an tsaron kasa da mamaki ba, in ji mai ba Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan, yayin wani jawabi da ya yi da safiyar jiya Lahadi a gidan talabijin na CNN. “Abin da ya nuna shi ne cewa Vladirimir Putin yana jin takaicin yadda dakarunsa ba sa samun irin ci gaban da ya yi tunani za su samu.”
Akalla mutane 35 suka mutu yayin da 134 suka jikkata da sanyin safiyar jiya Lahadi lokacin da Rasha ta harba makami mai linzami kan cibiyar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kasa da kasa, wani sansanin soji da ke yammacin Ukraine.
Wurin, wanda ba shi da nisa da Lviv, inda dakarun kungiyar tsaro ta NATO ke atisaye da sojojin Ukraine.
Dakarun NATO a Poland na da nisan kilomita 25, lamarin da ya sanya fargaba ko kuskuran da sojojin Rasha suka yi na iya sa yankin ya kara fadada.