Ko wani tasiri yakin Rasha da Ukraine ke da shi akan Najeriya, daya daga cikin kasashe masu arzikin man fetur da iskar gas da kuma kasar Noma a duniya?
Wani bincike da Bankin duniya da sauaran kafofin cinikayya na kasa da kasa suka fitar dai ya nuna cewa wannan yaki da kuma takunkumi da kasashen duniya suka kakaba wa Rasha da kuma kaurace wa kasar Ukraine mai fama da hare hare ko dakatar da harkokin yau da kullum da ita sakamakon mamayar kasar da Rasha ta yi, zai zame wa wasu kasashe gobarar titi. Musanman kasashe masu arzikin mai da iskar gas a duniya irinsu Najeriya da abokan cinikayyan kasashen biyu masu yaki za su karkato domin samun makamashi.
Ganin yadda Rasha ke kan gaba wajen samar da makamashi na mai da iskar gas ga kasashen Turai da Yamma, musanman Jamus, masana tattalin arziki a Najeriya na ganin da kyar ne Najeriya za ta ci gajiyar wannan garabasar, ganin yadda ita kanta Najeriya man da ta ke hakowa ya ragu matuka, kuma bata iya tace shi a cikin gida.
Haka kuma, akwai matsalar tsaro da yayi kama da yaki da tattalin arziki, wanda ta ke fuskanta, lamarin da kuma ke firgita masu saka jari a kowace kasa.
Dr Dauda Mohammed Kontagora na daya daga cikin masanan da ke da wannan ra'ayi, inda ya ce dole ne kasashen da za su ci gajiyar wannan yaki su kasance suma suna da karfin tattalin arziki da kuma tsaro; don haka yanayin da Najeriya ke ciki a yanzu babu yanda za ta ci gajiyar wannan yaki, sai ma dai a ce za ta yi asara ita ma, musanman batun shigo da alkama da kasar ta dogara wajen sarrafa biredi da fulawa na yin taliya da sauran abincin talakawa.
Wata asara da za a ce Najeriya ta tafka sakamakon wannan yaki dai shi ne yanda dubban daliban kasar da ke karatun likita suka dawo gida, ganin yadda suka maida kasar Ukraine wajen karatun aikin likita mai inganci kuma cikin sauki, ba kaman anan Najeriya da samun karatun likitan ke da wuya ba, da kuma uwa uba yajin aikin malaman jami'o'in da ya kassara ilimin manyan makarantun kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: