Ma'aikata da dalibai ‘yan asalin kasashen Afirka da ke neman ficewa daga Ukraine sakamakon mamayar da Rasha ta yi a kasar, na korafin cewa, ana hana su shiga motocin bas, jiragen kasa da hanyoyin ketara kan iyaka, yayin da aka baiwa 'yan kasar ta Ukraine fifiko.