Hukumar tsaron farin kaya ta Azerbaijan ta fada a yau Laraba cewa, tana gudanar da bincike kan "wani harin ta’addanci”, bayan da aka harbi wani dan majalisar dokoki mai tsattsauran ra’ayin kin jinin Iran, aka kuma yi masa rauni a gidansa.
A yau ne wata kotu a Amurka ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Solomon Ekunke Okpe, dan shekaru 31, hukuncin daurin shekaru hudu da wata daya a gidan yari, bisa samunsa da hannu a wata kungiyar masu aikata laifuka ta yanar gizo.
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta bayyana cewa shugabannin nahiyar Afrika na da gudunmuwar da zasu bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashen duniya.
‘Yan sandan Portugal sun harbe wani mutum da ake kyautata zato ya daba wa wasu mata biyu wuka har lahira a wata cibiyar Musulunci ta Ismaili Muslim Center da ke Lisbon, a cewar hukumomi a ranar Talata.
Fiye da bakin haure talatin da tara ne suka mutu sanadiyyar gobara a wata cibiyar ajiye bakin haure da ke arewacin Mexico a kusa da kan iyakar Amurka, in ji wani jami'i ranar Talata.
A ranar Litinin Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dage shirinsa na yin garambawul a bangaren shari’ar kasar sakamakon zanga-zangar da aka yi a kan titunan kasar.
A ziyararta ta mako guda zuwa nahiyar Afrika, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta isa kasar Ghana ranar Lahadi don tattaunawa kan batutuwa da yawa, ciki har da tattalin ariki.
Za a kammala taron a yammacin Juma’a 24 ga watan Maris inda a karshe mahalartan za su tsayar da shawarwarin da za su gabatar da su wa gwamnatocin kasashen uku.
Kazalika a kasar Qatar da ke makwabtaka da Saudiyyar, kwamitin duban wata ya sanar da cewa Alhamis ce ranar farkon watan na Ramadana.
Kotun har ila yau ta ba da izinin kama kwamishiniyar kare hakkin yara a ofishin shugaban kasar ta Rasha, Maria Alekseyevna Lvova Belova, wacce ita ma ake zargin ta da hannu a lamarin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Xi Jinping murnar sake lashe zabe karo na uku don wa’adin shekaru biyar a matsayin shugaban kasa kuma jagoran rundunar sojan China.
Domin Kari