An yi harbe-harbe a cikin wani gini da ‘yan cocin Jehovah’s Witness suke amfani da shi a birnin Hamburg da ke arewacin Jamus a yammacin jiya Alhamis, kuma mutane da yawa sun mutu wasu kuma sun jikkata, a cewari ‘yan sanda.
Hukumomin Najeriya sun mika wata ‘yar kasar da ake nema ruwa a jallo ga hukumomin Italiya wacce tun a shekarar 2010 ake nema ruwa a jallo, bayan hukuncin daurin shekaru 13 da aka yanke mata a Italiyar.
Takwas ga watan Maris din kowace shekara, rana ce da ake bikin mata ta duniya inda taken bana ya mai da hankali kan bukatar samar da daidaito a tsakanin jinsi.
Akalla bakin haure 43 ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwalen katako da suka yi cunkoso a ciki ya daki wasu duwatsun ruwa, ya kuma balle a kudancin Italiya kafin wayewar gari ranar Lahadi, in ji jami’an tsaron gabar tekun Italiya.
Jakadan kasar Canada a Najeriya Mr. Jammie Christoff ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a wani taron hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasar ta Canada, don karfafa matakan hadin kai na tunkarar kalubalen safarar mutane da yin kaura ba bisa ka’ida ba.
Vinicius Junior da Karim Benzema sun kara hada wa kungiyar Liverpool zafi a gasar Zakarun Turai, yayin da Real Madrid ta farfado inda ta yi nasara da ci 5-2 a filin wasa na Anfield.
A shekarar 2000 aka kebe ranar 21 ga Fabrairu, a matsayin ranar bukin harshen uwa ta duniya (IMLD).
Neymar bai samu karaya a idon sawunsa ba a wasan da Paris Saint-German ta doke Lille, amma sai ya jira karin gwaje-gwaje da aka yi masa don ganin ko ya samu rauni.
Kwallon farko da Brahim Diaz ya zura a raga tun watan Oktoban bara ta bai wa Milan nasara a kan Tottenham da ci 1-0, a wasan farko na zagayen ‘yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Karanci da rashin sabbin kudaden naira na haddasa rudami a kasuwar kan iyakar Najeriya da Nijar
Yadda Matasa Ke Ganin Radiyo Duk Da Amfani Da Kafafen Sadarwa Na Zamani Ke Yi Wajen Samun Labarai.
Domin Kari