Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar a ranar Lahadi, ya ce a karkashin shugabancin Xi, dangantaka tsakanin China da Najeriya, wadda aka fara tun a shekarar 1971 a lokacin da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiyya a hukumance, ta bunkasa cikin sauri a harkokin kasuwanci da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Shugaban ya yi imanin cewa makomar wannan kawancen da China zata ci gaba da bunkasa cikin sauri a fannonin soja, siyasa, kasuwanci, hada-hadar kudi, huldar mai da iskar gas, da ma hadin gwiwa a fannin sadarwa, noma da ababen more rayuwa da kuma masana’antu.
Shugaba Buhari ya yi wa gwamnatin China da jama’ar kasar fatan samun dorarren zaman lafiya, ci gaba da wadata a karkashin jagorancin shugaba Xi.