'Yan kasashen waje da dama, ciki har da Amurkawa da ‘yan kasar Canada sun makale a kasar Haiti, inda suke kokarin barin kasar mai fama da tashe-tashen hankula, inda kungiyoyin da ke adawa da gwamnati ke fafatawa da 'yan sanda, kuma tuni suka rufe filayen jiragen sama 2 na kasa da kasa na kasar.